Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-02 09:24:11    
Kasar Sin za ta yi kokarin kare masana'antunta daga illar da aka yi a cinikayya ta kawo

cri

A ran 1 ga wata, a birnin Guangzhou, ministan ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin Chen Deming ya bayyana cewa, bisa dokar kasar Sin da tsarin ka'idojin kungiyar WTO, gwamnatin kasar Sin za ta yi iyakacin kokarinta wajen kare kamfanonin da masana'antunta ta yadda za su samu kansu a yanayin ciniki na adalci da 'yanci a kasuwannin duniya.

Yayin da ke halatar bikin baje kolin kayayyakin shigi da fici na kasar Sin a karo na 106 da aka shirya a birnin Guangzhou Chen Deming ya bayyana cewa, kasar Sin tana daukar matakai a fannoni daban daban, don yaki da kariyar ciniki. Ban da haka kuma, ya ce, yanayin kasuwannin duniya sun fara farfadowa fiye da na shekarar da ta wuce da aka yin fama da matsalar kudi a duniya, gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar da manufofin da ta tsara wadanda suka dace da tsarin kungiyar WTO domin masana'antunta. Kuma ya kamata kamfanonin Sin su kara gaggauta aikin yin gyare-gyare da kara ingancin kayayyaki a yayin da yawan odar da kamfanonin ke yi ya karu, kuma wannan muhimmiyar hanya ce wajen kaucewa illar dake tattare da cinikayya.(Abubakar)