Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-02 09:20:02    
Masanan Sin da na kasashen waje sun tattauna kan dokokin Afirka da tarihin bunkasuwar zamantakewar al'umma

cri
An rufe taron tattaunawa na duniya kan dokokin Afirka da tarihin bunkasuwar zamantakewar al'umma a ran 1 ga wata a birnin Xiangtan na lardin Hunan dake tsakiyar kasar Sin. Masana fiye da dari daya daga kasashen Sin da Habasha da Mozambique da Faransa da Italy da kuma Belgium sun halarci taron.

Kungiyar nazarin tarihin Afirka ta kasar Sin ce ta shugabanci wannan taro, taken taron shi ne dangantaka tsakanin dokokin ciniki da muhallin zuba jari, da ka'idojin dokokin Afirka da dabi'u, da tsarin mulkin Afirka, da hulda tsakanin dokokin Afirka da zamantakewar al'umma da dangantaka tsakanin Afirka da sauran kasashen duniya. Wani jami'in ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin ya bayar da wani rahoton musamman game da halin da ake ciki a Afirka da yadda aka shirya taron ministoci na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a karo na 4.(Zainab)