Ranar 31 ga watan Oktoba, a nan birnin Beijing, ministan kiwon lafiya na kasar Sin Mista Chen Zhu ya bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar tana nan tana kokarin tsara wani shiri na yin rigakafi da yaki da cututtukan da suka dade a jikin dan Adam a cikin nan da shekaru 10 masu zuwa.
A yayin "Sin na daukar matakai-dandalin tattaunawa na kasa da kasa kan ciwon sukari", Chen Zhu ya bayyana cewa, kasar Sin zata yi iyakacin kokarin ci gaba da rage yawan mace-macen mata masu juna biyu a shekara ta 2015 da sulusani idan an kwatanta da na bara, da kara rage yawan mace-macen yara da shekarunsu suka yi kasa da 5, ta yadda za'a inganta lafiyar jikin Sinawa daga dukkanin fannoni.
Mista Chen Zhu ya kuma jaddada cewa, a halin yanzu, masana'antun kasar Sin na bunkasuwa cikin sauri, haka kuma zaman rayuwar jama'a na samun manyan sauye-sauye, hakan ya sa cututtukan da suka dade a jikin dan Adam sun zama manyan matsaloli ta fannin kiwon lafiya, shi ya sa kamata ya yi a karkata hankali kan yin rigakafin cututtuka.(Murtala)
|