Ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta bayar da wata sanarwa a ran 1 ga wata, inda aka yanke shawara ta karshe kan binciken da aka yi wa kayayyakin ADA da ake yin amfani da su wajen kera kayan roba, da ake shigo da su daga Amurka da kungiyar tarayyar Turai da Korea ta kudu.
Hukumar yin bincike ta ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta amince da cewa, kayayyakin ADA da aka shigo daga Amurka da kungiyar tarayyar Turai da Korea ta kudu sun zama kayayyaki masu araha da aka jibge su a kasar Sin, har sun kawo babbar illa ga masana'antun ADA na kasar Sin, wato wannan yana da nasaba da kayayyakin ADA da aka jibge su a kasar Sin. Sakamakon haka, ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta yanke shawara cewa, daga ranar 2 ga watan Nuwanba na shekarar 2009, kasar Sin za ta buga haraji irin na hana jibge kayayyaki da yawansa zai kai kashi 5 daga cikin dari zuwa kashi 35.4 daga cikin dari ga kayayyakin ADA da ake shigo daga Amurka da kungiyar tarayyar Turai da dai sauran kasashe da yankuna.(Danladi)
|