A ran 31 ga wata, Mr. Wen Jiabao, firayin ministan kasar Sin ya yi rangadin aiki a Asibitin Yara na Beijing, inda ya gai da likitoci da masu aikin jiyya da wadanda suka kamu da murar A H1N1. Ya bayyana cewa, kasar Sin tana da cikakken imani da karfi wajen shawo kan murar A H1N1 domin hana barkewar cutar a kasar, kuma za ta yi namijin kokarin rage yawan mutane masu kamuwa da cutar da su yi tsanani ko su mutu sakamakon cutar.
A kwanakin baya, an samu barkewar murar yau da kullum da murar A H1N1 tare a kasar Sin. Yawan yara masu kamuwa da mura da suka je Asibitin Yara na Beijing ya karu cikin sauri sosai.
Mr. Wen Jiabao ya ce, a cikin wasu watannin da suka gabata, kasar Sin ta samu nasara sosai wajen shawo kan murar A H1N1. Amma sabo da yanzu ana canja lokacin kaka da na sanyi, yawan 'yan ci rani ya yi yawa, an sake shiga hali mai tsanani wajen fama da murar A H1N1.
Mr. Wen Jiabao ya nemi hukumomi daban daban na matakai daban daban da su sanya aikin yin rigakafi da kuma shawo kan murar A H1N1 a wani muhimmin matsayi, kuma a kafa wani kwararan tsarin shawo kan murar. Mr. Wen ya kara da cewa, muddin an dauki matakai daidai, tabbas ne za a yi aikin shawo kan murar A H1N1 da kyau. (Sanusi Chen)
|