Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-31 16:52:30    
Kasar Sin ta nuna babbar hasala da kin amincewa da wata sanarwar EU

cri
A ran 30 ga wata, Mr. Ma Zhaoxu, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ya ce, kasar Sin ta nuna babbar hasala da kin amincewa da wata sanarwar da kungiyar tarayyar Turai, wato EU ta bayar.

A ran 29 ga wata, kasar Sweden, wadda ke shugabantar kungiyar EU yanzu ta wakilci kungiyar EU ta bullo da wata sanarwa, inda ta zargi kasar Sin domin kwanan baya kasar Sin ta harbi masu laifuffuka, 'yan kabilar Tibet biyu wadanda suka sa hannu a cikin matsalar da ta auku a birnin Lhasa na jihar Tibet a ran 14 ga watan Maris na bara, har ma kungiyar EU ta nemi kasar Sin da ta yi watsi da hukuncin kisa.

Game da wannan sanarwar kungiyar EU, Mr. Ma Zhaoxu ya ce, bangaren kasar Sin ya nuna babbar hasala da kin amincewa da wannan sanarwa. Matsalar da ta auku a ran 14 ga watan Maris a birnin Lhasa matsalar nuna karfin tuwo ce da rukunin Dalai ya mai da hankali sosai wajen shiryawa, kuma kungiyoyi da mutane na ciki da waje wadanda suke yunkurin neman 'yancin kan Tibet suka yi cikin hadin gwiwa. Hukumomin shari'a na kasar Sin sun bincike da kuma yanke hukunci kan mutane wadanda aka yi tuhumarsu da su sa hannu a cikin wannan matsala bisa dokokin kasar Sin a fili cikin adalci, kuma sun yanke hukuncin kisa kan wasu masu laifuffuka, wannan ikon mulki ne na kasar Sin a fannin daidaita harkokin cikin gida da na shari'a. Ba wanda yake da ikon tsoma baki kan harkokin cikin gida na kasar Sin. Haka kuma, bangaren kasar Sin ya tsaya tsayin daka kan matsayin kin amincewa da matakan tsoma baki kan harkokin cikin gida na kasar Sin da aka sauka a bakin batun hukuncin kisa. Kasar Sin ta nemi kungiyar EU da ta bi ka'idojin zaman daidai wa daida da girmamawa juna, kada ta ba da alamar kuskure ga wadanda suke neman 'yancin kan Tibet. (Sanusi Chen)