Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-31 16:14:36    
Hu Jintao ya taya murnar cika shekaru 60 da kafuwar cibiyar kimiyya ta kasar Sin

cri
A ran 30 ga watan Oktoba, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya aika wa cibiyar kimiyya ta kasar Sin wata wasika, inda ya taya murnar cika shekaru 60 da kafuwarta.

Hu Jintao ya nuna cewa, a halin da ake ciki yanzu a duniya, ana kokarin samun babban ci gaba da sauye-sauye iri na "juyin juya hali" bisa sabbin fasahohi da kimiyya na zamani. Kasashen duniya suna kuma kara mai da hankali kan yadda za a iya yin amfani da fasahohin zamani da ilmin kimiyya wajen neman ci gaba.

Haka kuma, Mr. Hu yana fatan cibiyar kimiyya ta kasar Sin ta yi kokarin samun sabbin fasahohin zamani masu inganci, kuma ta bayar da gudummawarta kamar yadda ake fata lokacin da ake kokarin raya kasar Sin da ta zama kasa mai karfin kirkira, kuma ta bayar da karin gudummawa wajen ciyar da fasahohin zamani da kimiyya gaba a kasar Sin da kuma neman samun sabuwar nasarar raya zaman al'umma mai matsakaicin karfi daga dukkan fannoni a kasar. (Sanusi Chen)