Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-31 15:56:43    
Rukuni na 2 na rundunar kiyaye zaman lafiya da Sin ta tura zuwa Sudan a karo na 5 ya dawo gida

cri
Ran 30 ga wata, sojoji 215 na rukuni na 2 da ke cikin rundunar kiyaye zaman lafiya da kasar Sin ta tura zuwa kasar Sudan a karo na 5 sun dawo kasar Sin tare da samun babban yabo.

Kafinsu kuma, wasu 220 na rukuni na farko sun dawo gida ran 22 ga wata.

Rundunar kiyaye zaman lafiya ta kasar Sin a karo na 5 ta hada sojoji injiniyoyi da sojojin da ke kula da yin jigilar kaya da sojoji likitoci. Bayan da aka girke su a Sudan a watan Febrairu a bana, sun kammala ayyukan fadada filayen jirgin sama, da bai wa sauran hukumomin kiyaye zaman lafiya a shiyyar da suke ciki isasshen ruwa, da yin jigilar kayayyaki, da ba da magani ga mazauna wurin da dai sauransu. Sun samu babban yabo daga wajen hukumomin wurin da mazauna wurin gami da Majalisar Dinkin Duniya. Dukkan hafsoshi da sojoji 435 na Sin sun samu lambar yabo ta kiyaye zaman lafiya daga Majalisar Dinkin Duniya, a yayin da rassa 3 na rundunar da mutane 13 suka samu lambar yabo ta musamman daga kwamandan rundunar kiyaye zaman lafiya da Majalisar Dinkin Duniya ta jibge a Sudan.(Tasallah)