Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-30 21:04:40    
Kasar Sin ta tabbatar da manufofi 8 da ta tsara kan Afrika

cri

Jami'an ma'aikatar harkokin waje da na ma'aikatar kasuwanci na kasar Sin sun bayyana a ran 30 ga wata cewa, a gun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa na hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afrika na shekarar 2006, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya sanar da manufofi 8 da Sin ta tsara kan Afrika don yin hadin gwiwa. Yanzu, an riga an tabbatar da wadannan manufofi 8.

A fannin kara samar da tallafi ga Afrika, ya zuwa karshen watan Satumba na shekarar 2009, an riga an tabbatar da kashi 90 cikin dari na wadannan manufofi, kuma ya zuwa karshen wannan shekara, za a cika alkawarin da yawansa ya ninka sau daya idan aka kwatanta da shekarar 2006.

A fannin yafewa Afrika bashi, gwamnatin kasar Sin ta kulla yarjejeniyoyin yafewa kasashen Afrika 33 mafi fama da talauci basussukan da ta ba su.

A fannin kara zuba jari, ya zuwa karshen shekarar 2008, kasar Sin ta zuba jari ga kasashe da yankuna 49 na Afrika, wanda yawansa ya kai dalar Amurka biliyan 26.

A gun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa na hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika, Hu Jintao ya sanar da kafa yankuna 3 ko 5 na hadin gwiwa na tattalin arziki da ciniki a Afrika. Yanzu, an fara gina wadannan yankuna a kasashen Zambiya da Mauritius da Nijeriya da Masar da Habasha da dai sauransu.(Lami)