Daga ran 28 zuwa 30 ga wata a lardin Shandong, firaministan majalisar gudanarwa ta kasar Sin Wen Jiabao ya dudduba sakamakon da aka samu wajen bunkasa harkokin zaman al'umma. Ya ce, dole ne a kara dora muhimmanci kan aikin bunkasa tattalin arziki da zaman al'umma tare. Hakan zai sa a iya kawo karshen rikicin hada-hadar kudi na duniya da samun bunkasuwar tattalin arziki yadda ya kamata.
Wen Jiabao ya ziyarci hukumomin jiyya na birane da na kauyuka. Inda ya jaddada cewa, yin gyare-gyare kan tsarin harhada magunguna da kiwon lafiya muhimmin aiki ne, ya kamata a kara kyautata aikin ba da jiyya a kauyuka da gundumomi daban daban.
Bayan da Wen Jiabao ya ziyarci wata karamar cibiyar ba da hidima ga 'yan kwadago ta birnin Ji'nan ya ce, ya kamata a kyautata tsarin ba da tabbaci ga zaman al'umma musamman ma inshorar rashin guraban aikin yi da inshorar kudin fansho da inshorar jiyya don ba da tabbaci ga zaman rayuwar jama'a.(Lami)
|