Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-30 15:58:53    
Sin ta gudanar da matakai wajen cika alkawarin da ta yi na soke basussukan da take bin ga kasashen Afrika

cri
A ranar 30 ga wata, bisa labarin da manema labarun suka samu daga ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin, an ce, bayan da gwamnatin Sin da kasar Somaliya suka kulla yarjejeniyar soke basussuka tsakaninsu, kasar Sin ta riga ta soke basussuka 6 da take samarwa ga kasar Somaliya ba tare da kudin ruwa ba, kana, Sin ta riga ta cika alkawarin da ta yi a wajen taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika domin soke basussukan da take bi ga kasashen Afrika.

A gun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika da aka yi a shekarar 2006, gwamnatin Sin ta sanar da daukar matakai 8 wajen kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, ciki har da soke dukkan basussukan da kasar Sin take bi ga kasashen Afrika mafi talauci da wadanda suka kulla dangantakar diplomasiyya da kasar Sin da ba su biya ba kawo karshen shekarar 2005.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, domin gudanar da wadannan matakai, a cikin shekarar 2006, bi da bi ne kasar Sin ta kulla yarjejeniyoyi da kasashe 32 wajen soke basussuka, a gaba daya dai, Sin ta soke basussuka 150.(Bako)