Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-30 15:17:53    
Cibiyar nazarin kimiyya ta kasar Sin za ta yi kokari don zama cibiyar nazarin kimiyya mafi karfi na duniya a shekarar 2020

cri
A ran 30 ga wata, a birnin Beijing, shugaban cibiyar nazarin kimiyya ta kasar Sin Lu Yongxiang ya bayyana cewa, cibiyar nazarin kimiyya ta kasar Sin za ta yi kokari wajen warware manyan batutuwan da ke dangane bunkasuwar kasar, don inganta karfin nazarin kimiyya na kasar Sin, da yin kokari don zama cibiyar nazarin kimiyya mafi karfi na duniya a shekarar 2020.

Malam Lu Yongxiang ya bayyana haka a wajen bikin taya murnar cika shekaru 60 da kafuwar cibiyar nazarin kimiyya ta kasar Sin da aka shirya a ran nan. Kuma ya bayyana cewa, a cikin shekaru 60 da suka wuce, cibiyar nazarin kimiyya ta kasar Sin ta samu sakamako da yawa a fannonin yin nazarin manyan ayyukan yau da kullum da yin binciken fasahohi bisa manyan tsare-tsare. Kuma ta ci nasara wajen yin binciken na'urar kwamfuta da hanyar jirgin kasa ta Qinghai-Tibet da aikin tafiyar kumbon da ke dauke da 'yan sama jannati da sauransu, kuma cibiyar ta ba da muhimmiyar gudumawa ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar.(Abubakar)