Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-30 11:07:45    
Musulman kasar Sin za su je Mecca na kasar Saudiya don yin aikin haji

cri
Daga ran 30 ga wata zuwa ran 17 ga watan Nuwamba, musulman kasar Sin kimanin dubu 12 da dari 7 za su je Mecca na kasar Saudiya don yin aikin haji. Hakan ya kasance fi yawa a tarihi.

Manema labaru sun samu labari daga kungiyar addinin Musulunci ta kasar Sin cewa, musulman da za su yi aikin haji za su dauki jiragen sama 41 wadanda za su tashi daga birane biyar wato Lanzhou, da Urumqi, da Kunming, da Yinchuan, da kuma Beijing zuwa Mecca. Bayan sun gama aikin haji, daga ran 3 ga watan Disamba zuwa ran 21 ga watan Disamba, za su komo bi da bi.

An ba da labari cewa, a shekarar bana, musulman da za su yi aikin haji sun zo daga larduna da birane kimanin 27 na babban yankin kasar Sin, ciki har da kabilu goma dake bin addinin musulunci wato kabilar Hui da ta Uygur, da Kazak, da kuma Uzbek da dai sauransu.

Yayin da ake fuskantar annobar cutar mura mai nau'in A(H1N1) a bana, don tabbatar da yin aikin haji lami lafiya, gwamnatin kasar Sin za ta yi allurar rigakafin cutar mura mai nau'in A(H1N1) wa duk musulman da za su yi aikin haji da ma'aikata, kuma za ta tura rukunin masana na musamman don rigakafin cutar, kana za ta dauki matakai da dama don rigakafin cutar, ta yadda za ta biyo bukatun musulmai.

A halin yanzu, a Saudiya, rukunin kula da aikin haji ya rigaya ya shirya abubuwa kamar su abinci da dakin kwana, da kiwon lafiya da rigakafin cututtuka, da tsaro da dai sauransu.(Asabe)