Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-29 18:53:13    
Dandalin tattaunawa na hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika ya kara jawo hankalin duk duniya ga Afrika

cri

Daga ran 8 zuwa 9 ga watan Nuwamba a birnin Sharm El Sheikh, za a bude taron ministoci na 4 na dandalin tattaunawa na hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika. Sakataren kwamitin shirya taron kuma daraktan sashen Afrika na ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Zhang Ming ya furta cewa, dandalin tattaunawa na hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika ya kara jawo hankalin duk duniya ga Afrika, kasar Sin ta yi alfahari kan haka.

Zhang Ming ya ce, taron ministoci na 4 na dandalin tattaunawa na hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika muhimmin taro ne bayan da aka yi taron koli na dandalin tattaunawa na Beijing a shekarar 2006, kasar Sin za ta kyautata manufofi 8 da ta tsara a gun taron koli na Beijing don tabbatar da kara samun bunkasuwar ayyukan hadin gwiwarsu, da kuma gudanar da matakan da abin ya shafa da firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya gabatar a watan Satumba na shekarar bara a gun taron koli na burin samun bunkasuwa da MDD ta tsara a shekarar 2000.(Lami)