A ran 29 ga wata a nan birnin Beijing, an kaddamar da taron tattaunawa na kwanaki 2 kan yaki da talauci da kula da harkokin kananan yara na duniya.
An gudanar da taron a karkashin jagorancin asusun nazarin bunkasuwa na kasar Sin, inda aka yi kira ga gwamnatoci da su sa lura kan lafiyar kananan yara da ba da ilmi gare su, da kawar da talauci daga tushe, da samar da sharadi mai adalci kan harkokin kananan yara a yankuna masu talauci, don hana yaduwar talauci da samun adalci da bunkasuwa mai dorewa a zamantakewar al'umma.
Masu samun lambar yabo ta Nobel a fannin tattalin arziki Amartya Sen da Joseph Stiglitz da masana daga kungiyoyin duniya kamar hukumar shirin raya kasa ta MDD wato UNDP da asusun tallafawa yara na MDD wato UNICEF za su tattauna tare da shugabannin ma'aikatar ba da ilmi da ta kiwon lafiya na kasar Sin da kuma ofishin ba da taimako ga masu fama da talauci na majalisar gudanarwar kasar Sin kan tsarin samar da abinci mai gina jiki a makaranti da aikin kula da lafiyar kananan yara da kuma ba da ilmi gare su don neman matakan yaki da talauci a kasar Sin.(Zainab)
|