Bisa labarin da hukumar kiwon lafiya ta birnin Beijing ta bayar a ran 28 ga wata da dare, an ce, wani dalibin jami'ar koyon ilmin sararin samaniya ta birnin Beijing ya mutu a sakamakon cutar murar A(H1N1). Ya zuwa yanzu, yawan mutanen da suka mutu a sakamakon cutar murar A(H1N1) a babban yankin kasar Sin ya haura zuwa 4. A fuskantar mawuyancin hali wajen yaduwar cutar, a kwanan baya, kasar Sin ta daidaita matakan hana yaduwar cutar, bisa tushen kara daukar matakan yin rigakafin cutar murar A(H1N1), za a kara yin jinya ga masu fama da cutar mai tsamari.
A kwanan baya, ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin ta yi kira ga yankuna daban daban da su kara mai da hankali a kan mutanen musamman, da kara karfi wajen gano masu fama da cutar murar A(H1N1) mai tsamari jiyya. A sa'i daya kuma, ta yi kira ga hukumomi na matakai daban daban da su kafa kungiyoyi masu yaki da cutar mai tsamani jiyya, da daukar matakai daban daban wajen yi musu kariya da cutar mai tsamani, da inganta na'urora asibitoci, da yin kokari wajen yi musu kariya kan cutar mai tsamani.Bisa labarin da aka bayar, an ce, yanzu ana gudanar da ayyukan yi allurar hana kamuwa da cutar murar A(H1N1) a yankuna daban daban na kasar Sin, a birnin Beijing da lardunan Jilin da Shandong da Mongoliya ta gida da Guangxi da Fujian da Jiangxi da sauransu, an fara yin allurar ga mutane musamman.(Abubakar)
|