A ran 28 ga wata da dare, agogon Beijing, an shirya bikin kammala gasar wasannin motsa jiki ta Jamhuriyar Jama'ar Sin a karo na 11 a birnin Ji'nan, babban birnin lardin Shandong dake gabashin kasar.
Wannan ce gasar wasannin motsa jiki mafi kasaita kuma mafi nuna gwaninta a kasar Sin. An fara wannan gasa ne a hukunce a ran 16 ga watan.
Haka kuma, za a yi gasar wasannin motsa jiki ta duk kasar Sin a karo na 12 ne a lardin Liaoning da ke arewa maso gabashin kasar Sin a shekara ta 2013. (Sanusi Chen)
|