Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-28 16:15:23    
Aniyar masaya na kasar Sin ta kai sabon matsayi a cikin watanni uku da suka gabata idan an kwatanta da na shekaru biyu da suka wuce

cri
Bisa sakamakon binciken da mashahurin kamfanin binciken kasuwa na duniya wato kamfanin Nielsen ya bayar a ran 28 ga wata, an ce, sakamakon samun kudin shiga yadda ya kamata da karuwar aniyar samun guraban aikin yi, aniyar masaya na kasar Sin ta kai sabon matsayi a cikin watanni uku da suka gabata, Hakan ya fi kyau tun daga tsakiyar shekarar 2007.

Binciken aniyar masaya na kasar Sin da kamfanin Nielsen ya yi ya fi girma a cikin ire-iren bincike kamar haka. A wannan karo, kamfanin ya binciki masaya fiye da dubu 3 da dari 4 na birane da kauyuka na mataki daban daban, makasudinsa shi ne ganin matsayin aniyar masaya na kasar Sin, da hanyoyin da su kan bi yayin da suke yin sayayya, da kuma yin hasashen yanayin saye-saye a nan gaba. Sakamakon binciken ya bayyana cewa, aniyar masaya na kasar Sin daga watan Yuli zuwa Satumba na bana ta karu da kashi 6 cikin dari har ta kai kashi 101 cikin dari idan an kwatanta ita daga watan Afrilu zuwa Yuni. A cikinsu, masaya na birane manya da matsakaita sun fi nuna aniya, kuma aniyar masaya na yankunan tsakiya da na yammacin kasar ta fi samun karuwa.(Asabe)