A ran 27 ga wata, wani jami'in ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya bayyana cewa, tun daga abkuwar matsalar kudi ta duniya, kasar Sin tana ci gaba da kara zuba jari ga kasashen Afirka.
Ya zuwa karshen shekarar 2008, yawan jarin da kasar Sin ta zuba wa kasashe da yankuna 49 na Afirka ya kai dala biliyan 26.
Gwamnatin kasar Sin tana matsa kaimi ga kamfanonin kasar da su shiga ayyukan ginaa manyan gine-gine na kasashe daban daban na Afirka. Kuma ayyukan da kasar Sin ta gina a kasashen Afirka sun bi bukatar bunkasuwar tattalin arzikin kasashen Afirka da zaman rayuwar jama'a. Ban da haka kuma, yayin da kamfanonin kasar Sin suka yin hadin gwiwa da zuba jari ga kasashen Afirka, sun yi kokari wajen samar da guraben aiki yi, da kara yin korar da mazauna, da mai da hankali a kan aikin horar da manajoji, da yin kokari wajen sayi danyun kayayyaki, da sayar da fasahohi, don tabbatar da amfana da moriyar juna da bunkasuwa tare a tsakanin Sin da kasashen Afirka.(Abubakar)
|