Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-27 18:34:53    
Masu aikin jiyya 6 na Sin sun samu lambobin yabo na Nightingale

cri

A ran 27 ga wata a nan birnin Beijing, an bude taron wakilan kungiyar Red Cross na kasar Sin a karo na 9. Shugaban kasar Sin kuma babban shugaban kungiyar Red Cross ta kasar Hu Jintao ya halarci bikin bude taron, kuma ya ba da lambobin yabo ga masu aikin jiyya 6 na kasar Sin da suka samu lambar Ninghtingale ta 42.

An kafa kungiyar Red Cross ta kasar Sin a shekarar 1904. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, a cikin shekaru 5 da suka gabata, kungiyar ta tattara kayayyaki da kudi da yawansu ya kai RMB biliyan 29, kuma mutane miliyan 120 sun ci gajiyarsu.

Mataimakin firaministan kasar Sin Hui Liangyu ya furta a gun bikin cewa, kungiyar Red Cross ta kasar Sin za ta hada ka'idar kungiyar Red Cross ta duniya da ra'ayin kirki na gargajiya na Sin wato tallafawa matalauta da girmama tsoffi da kokarin ceton mutanen da suke fama da ciwace-ciwace bisa hakikanin halin da kasar Sin ke ciki don kara karfinta na ceton mutane da kara tasirin da kungiyar ta ke da shi ga al'umma.(Lami)