Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-27 15:01:50    
Kasar Sin za ta kara karfin kiyaye asalin ruwan sha

cri
A ran 27 ga wata, a birnin Shenyang dake arewacin kasar Sin, mataimakin ministan kiyaye muhalli na kasar Sin Zhang Lijun ya bayyana cewa, a mataki na gaba, kasar Sin za ta ci gaba da kara karfin kiyaye asalin ruwan sha, kana za ta mai da hankali wajen hana gurbatar ruwa sakamakon amfani da manyan karafa.

A gun wani taro game da kiyaye ruwan sha da aka yi a ran nan, mista Zhang Lijun ya ce, kasar Sin za ta kara karfin kiyaye muhalli na yankin asalin ruwan sha, kuma za ta tsaya kan kawar da haramtattun gine-gine da ayyukan wadanda mai yiyuwa ne su iya gurbata asalin ruwa a wannan yanki; bugu da kari, za ta kara karfin tinkarar matsala cikin gaggawa, da kimanta matsalar gurbata muhalli; dadin dadawa, za ta yi amfani da kafofin yada labaru don karfafa wayar da kan jama'ar kasar a fannin kiyaye asalin ruwan sha.(Asabe)