Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-27 12:55:49    
Sana'ar masana'antu ta samu farfado a cikin watanni 9 da suka wuce na bana

cri
Bisa alkaluman da ma'aikatar masana'antu da sadarwa ta kasar Sin ta bayar a ran 27 ga wata, an ce, a cikin watanni 9 da suka wuce na bana, yawan kudin da aka samu daga sana'ar masana'antu ya karu da kashi 8.7 cikin kashi 100 bisa na makamancin lokaci na bara, tun daga watan Yuli zuwa watan Satumba saurin karuwa ya karu sosai, a ko wace wata, yawan karuwar ya wuce kashi 1 cikin kashi 10 bisa na makamancin lokaci na watan jiya, sana'ar masana'antu ta samu farfadowa da a zo a gani.

A cikin watanni 9 da suka wuce na bana, sana'o'in kayayyakin gini da magunguna da masana'antu sun fi sauri karuwa, kuma yawan karuwar ya wuce kashi 10 cikin kashi 100. Kuma sana'ar masana'antu na yankunan yammacin kasar Sin ta fi na yankunan gabashin kasar da na tsakiyar kasar saurin karuwa. A sa'i daya kuma, yawan kudin da kamfanoni suka samu ya karu, yawan wutar lantarki da yawan kayayyakin da aka yi sufurinsu sun karu sosai, kuma yawan jarin da aka zuba wa sana'ar masana'antu a cikin watanni 9 da suka wuce na bana ya karu da kashi 25 cikin kashi 100.(Abubakar)