Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-26 18:54:40    
Ana girmama rayuka da mutuncin jama'a bisa hukuncin da aka yanke kan matsalar da ta auku a ran 5 ga watan Yuli

cri
A ran 12 da ran 15 ga watan Oktoba, matsakaiciyar kotun jama'a ta birnin Urumqi ta sanarwa jama'a hukuncin da ta yankewa masu laifi su 21 wadanda suke da hannu cikin matsaloli 6 da suka auku a ran 5 ga watan Yuli na shekarar da ake ciki a birnin Urumqi. Bayan da kafofin watsa labaru suka yada wannan labari, wasu baki 'yan kasuwa da kwararru na kasashen waje da suke zaune a jihar Xinjiang mai cin gashin kanta sun bayyana cewa, an yanke hukunci kan matsalar da ta auku a ran 5 ga watan Yuli daidai da dokoki, hakan ba kawai nauyi ne da ke kan gwamnati ba, hakki ne da ke kiyaye da kuma girmama rayuka da mutunci na jama'a.

Malam Faiz Mohammud Hass, shugaban kungiyar 'yan kasuwa ta kasar Afghanistan da ke kasar Sin ya ce, an yanke wa masu laifi hukunci daidai da doka, wannan al'amari ne da ke faruwa a duk fadin duniya sabo da wannan nauyi ne da ke kan kowace kasa.

Wani mai suna Michael, dan kasar Canada wanda ke koyarwa a jami'ar Xinjiang ya ce, an yanke hukunci ne domin girmama da kuma mutunta rayukan da aka wulakanta. Ya ce, wasu kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya ba su bayyana gaskiyar labaru ba, sakamakon haka, aka kasa gane gaskiyar lamari game da jihar Xinjiang. A matsayin wani bakon da ke zaune a jihar Xinjiang, "ina da nauyin sanar wa sauran kasashen duniya wata hakikanin jihar Xinjiang wadda ke cike da kyakkyawar makoma." (Sanusi Chen)