Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-26 21:33:31    
Kasar Sin za ta ba da karin taimako ga Afirka

cri

Ran 26 ga wata, bisa labarin da muka samu daga ma'aikatar harkokin ciniki ta kasar Sin, an ce, kasar Sin za ta fara cika alkawarinta na ba da karin taimako ga kasashen Afirka a karshen shekarar bana.

Kasar Sin ta yi wannan alkawari ne a yayin taron koli na Beijing na dandalin hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen Sin da Afirka a watan Nuwamba na shekarar 2006 cewa, kasar Sin za ta ninka taimakon da take baiwa kasashen Afirka a shekarar 2006 kafin shekarar 2009.

Bisa labarin da muka samu, an ce, ya zuwa karshen watan Satumba na shekarar bana, kasar Sin ta riga ta gudanar da kashi fiye da 90 cikin 100 wajen cika alkawarinta.

Wannan alkawari ya hada da kasar Sin ta horar da mutanen kasashen Afirka dubu 15 a fannoni daban daban, kasar Sin ta aika da kwararru masu ilmin aikin gona 100 zuwa kasashen Afirka, da kafa cibiyoyin nuna fasahohin aikin gona 10, da ba da taimakon ginawar asibitoci 30, da ba da taimakon kudi na RMB yuan miliyan 300 domin yin rigakafi da kawar da ciwon zazzabin sauro., da gina makarantu 100 a kauyuka ga kasashen Afirka. An ce, ya kamata kasar Sin za ta cika wannan alkawari kafin karshen shekarar da muke ciki. [Musa Guo]