Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-26 14:32:13    
Yawan makamashin da kasar Sin ta sarrafa a cikin watanni 9 da suka wuce na bana ya karu da kashi 9 cikin kashi 100

cri
A ran 26 ga wata, a birnin Beijing, shugaban sashen gudanarwa na hukuma mai kula da makamashi ta kasar Sin Zhou Xian ya bayyana cewa, yawan makamashin da kasar Sin ta sarrafa a cikin watanni 9 da suka wuce a bana ya kai ton biliyan 2.01, wanda ya karu da kashi 9 cikin kashi 100 bisa na makamancin lokaci na bara.

A gun taron manema labaru da hukumar ta shirya a ran nan, Zhou Xian ya bayyana cewa, tun daga watan Afrilu zuwa na Yuni, tattalin arziki na kasar Sin ya samun farfado sosai musamman ma tattalin arzikin masana'antu, sabo da haka, yawan bukatun makamashi ya karu sosai. Tun daga watan Yuli, saurin bunkasuwar tattalin arziki na kasar Sin ya karu, sabo da haka, sana'ar makamashin kasar Sin ta ci gaba da samun bunkasuwa.

Zhou Xian ya bayyana cewa, halin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ya fi zaton da aka yi a farkon shekarar bana, an yi hasashen cewa, a cikin karshen watanni 3 na shekarar bana, tattalin arzikin makamashi zai ci gaba da samun bunkasuwa.(Abubakar)