Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-25 20:30:23    
An rufe ajin nazarin rigakafin cin hanci da al'amubazzaranci a karo na biyu a Beijing

cri
A ran 25 ga wata a nan birnin Beijing, an rufe ajin nazarin batun rigakafin cin hanci da al'amubazzaranci a kasashe masu tasowa a karo na biyu. Mr. Ma Kai, wakilin majalisar gudanarwa ta kasar Sin kuma babban sakataren majalisar ya halarci bikin rufe wannan aji, inda ya mika wa wakilan mahalarta ajin takardun sheda halartar wannan ajin.

Lokacin da yake ganawa da wasu wakilan mahalarta ajin da jakadun wasu kasashe da ke nan kasar Sin kafin bikin rufe ajin, Mr. Ma Kai ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin tana son raya huldar aminci a tsakaninta da hukumomin yaki da cin hanci da al'amubazzaranci na sauran kasashe masu tasowa bisa ka'idojin girmamawa juna da kokarin neman hakikanin ci gaba. Kuma tana son yin koyi da juna da kara yin hadin gwiwa a tsakaninsu domin neman sabbin hanyoyin yaki da cin hanci da al'amubazzaranci.

An bude wannan aji ne a karo na biyu tun daga ran 19 ga watan Oktoba. Wakilai 34 da suka zo daga kasashen Afirka da Asiya da kasashen nahiyar Amurka ta tsakiya sun halarci wannan aji. (Sanusi Chen)