Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-25 16:25:38    
Kasar Sin ta kara saurin samar da abinci mai inganci

cri
Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin ya samu a gun bikin baje koli na abinci mai inganci da ake yi a birnin Yantai na lardin Shandong a karo na 10, an ce, ya zuwa karshen watan Satumba na shekarar da ake ciki, yawan kamfanonin da suke sarrafa abinci mai inganci a duk kasar Sin ya riga ya kai kusan 6500, kuma yawan ire-iren abinci mai inganci da suke sarrafawa ya kai kusan dubu 18. Yanzu sun riga sun yi rajistar alamunsu a kasashen Japan da Amurka da Rasha da Britaniya da Faransa da Portugal da Finland da kuma yankin Hongkong na kasar Sin.

Bisa kididdigar da ma'aikatar aikin gona ta kasar Sin ta bayar, an ce, ya zuwa karshen shekara ta 2008, yawan abinci mai inganci da aka samar a duk kasar Sin ya kai ton miliyan 90, kuma yawan kudin da aka samu domin fitar da abinci mai inganci ga kasashen waje ya kai dalar Amurka biliyan 2 da miliyan dari 4. (Sanusi Chen)