Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-24 20:26:44    
Masana'antun kayan musulmai na zamani a birnin Yinchuan na jihar Ningxia ta kasar Sin sun hakaba kasuwa bisa babban mataki

cri

Bisa labarin da muka samu daga hukumar da ke kula da harkokin kididdga ta birnin Yinchuan ta jihar Ningxia ta kasar Sin a 'yan kwanakin baya, an ce, a cikin farkon watanni 9 na shekarar bana, yawan kudaden shiga da birnin Yinchuan ya samu daga masana'antun abincin musulmai, da kayan kiwon lafiya da kuma sauran kayayyakin dangane da musulmai ya kai kudin Sin Yuan biliyan 4 da miliyan 214, wanda ya karu da kashi 11.1 daga cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara, wannan ya bayyana cewa, masana'antun kayan musulmai na zamani a birnin Yinchuan na jihar Ningxia ta kasar Sin sun hakaba kasuwa bisa babban mataki.

Bisa labarin da muka samu, an ce, a halin yanzu, birnin Yinchuan ya riga ya kafa yankunan masana'antun abinci da kayan musulmai da dama kamar yankin masana'antu na Desheng da ke gundumar Helan da dai sauransu. A cikin wadannan yankuna, ana iya gudanar da ayyukan samar da kaya bisa babban mataki, kuma bisa ka'ida daya.(Danladi)