Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-24 20:25:27    
Kasar Sin ta kara kwarewa wajen kare ikon mallakar dabi

cri

Shugaban babbar hukuma mai kula da madaba'a da watsa labarai ta kasar Sin, kuma darektan hukumar da ke kare ikon mallakar dabi ta kasar Sin Mr. Liu Binjie ya bayyana a ran 24 ga wata a birnin Beijing cewa, a cikin shekaru fiye da 30 tun da kasar Sin ta fara yin gyare gyare a gida da bude kofa ga duniya har zuwa yanzu, kasar Sin ta kara kwarewarta wajen kare ikon mallakar dabi, a halin yanzu ta iya biya bukatar ka'idojin duniya, haka kuma cikin yakini ne, kasar Sin ta dauki nauyin da ke bisa wuyanta a harkokin duniya.

Mr. Liu ya yi wannan bayani ne a yayin da yake bayar da wani jawabi a taron baje koli na ikon mallakar dabi na duniya a karo na biyu, wanda aka shirya ran nan. Liu ya ce, a nan gaba kasar Sin za ta ci gaba da karfafa kwarewarta wajen kare ikon mallakar dabi, da kara kyautata tsarin dokokin da abin ya shafa, za ta mai da hankali sosai kan daidaita sababbin mataloli da aka samu daga fasahohin zamani kamar internet. Liu ya ci gaba da cewa, kasar Sin za ta kago wani kyakkyawan yanayi ga yin musanya da hadin hai a fannonin tattalin arziki da cinikayya a tsakaninta da kasashen waje.(Danladi)