Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-24 17:07:37    
An yi taron dandalin tattaunawa kan bunkasuwar ayyukan zirga-zirgar kayayyaki da sayen kayayyaki tsakanin Sin da Afrika a lardin Shandong

cri
A ranar 24 ga wata, an yi taron dandalin tattaunawa kan bunkasuwar ayyukan zirga-zirgar kayayyaki da sayen kayayyaki a karo na farko na shekarar 2009 a birnin Longkou na lardin Shandong dake gabashin kasar Sin.

Dalilin da ya sa aka shirya taron shi ne, domin kafa wani dandawalin yin cudanyar cinikayya tsakanin Sin da kasashen Afrika, kana da tattauna kan ayyukan jigilar kayayyaki da sayen kayayyaki a yayin da ake yin cinikayya da zuba jari tsakanin Sin da kasashen Afrika, da kuma rage yawan kudi da aka kashe wajen ayyukan biyu, kazalika kuma, za a yi nazari kan habaka hanyoyin yin cudanya tsakanin masana'antun jigilar kayayyaki tsakanin Sin da kasashen Afrika, ta yadda za a ba da sharadi ga kara hadin kan cinikayya tsakanin bangarorin biyu.

A gun taron dandalin tattaunawar da za a shafe kwanaki biyu ana yinsa, jami'ai na gwamnati, da na masana'antu, da kuma kwararru da suka fito daga kasashen Sin, da Angola, da Kongo Brazzaville, da Kenya, da dai sauransu za su yi jawabi kan batuttuwan kalubalolin da ake fuskanta a yanzu ta fuskar matsalar kudi, da hadin kan tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afrika, da kuma nazarin kasuwar jigilar kayayyaki a teku, da dai sauransu. (Bilkisu)