 Ranar 23 ga wata, a nan birnin Beijing, shugaban kwamitin dindindin na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Mista Wu Bangguo ya gana da takwaran aikinsa na kasar Kenya Kenneth Marende. Mista Wu ya bayyana cewa, kasar Sin na maida hankali sosai kan bunkasa dangantaka a tsakaninta da kasashen Afirka, ciki kuwa har da Kenya, yana fatan samun habaka hadin-gwiwa da samun moriyar juna tsakanin Sin da Afirka, da tinkarar rikicin hada-hadar kudi na duniya tare, gami da kokarin raya huldar dake tsakanin kasashen Sin da Kenya, da ta tsakanin Sin da kasashen Afirka baki daya zuwa sabon matsayi.
Wu Bangguo ya ce, yana fatan bangarorin biyu zasu ci gaba da yin mu'amala da cudanya tsakanin manyan jami'ansu, da inganta yin musayar ra'ayoyi ta fannonin mulkin kasa da gudanar da harkokin siyasa, da karfafa ayyukan cude-ni-in-cude-ka, ta yadda za'a sanya sabon kuzari ga bunkasuwar huldodin Sin da Kenya daga dukkanin fannoni.
A nasa bangare kuma, Marende ya nuna cewa, Kenya na fatan yin koyi da nasarorin da Sin ta samu ta fannin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'umma, da inganta hadin-gwiwar kasashen biyu a fannonin ayyuna gona, da sha'anin yawon shakatawa, gami da ilmantarwa.(Murtala)
|