Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-23 11:05:57    
An fara watsa labaru a hukunce a tashar Beibu Bay dake jihar Guangxi ta Sin

cri
A ran 23 ga wata a birnin Nanning na jihar Guangxi ta Sin, an soma watsa labaru a hukunce a Beibu Bay dake wannan jihar bisa jagorancin gidan rediyon kasar Sin da gidan rediyon mai watsa labaru ga kasashen waje na jihar Guangxi tare, kuma wannan ce tashar FM ta farko a Sin ta watsa labarun duniya zuwa shiyya-shiyya.

A gun bikin budewar, shugaban gidan rediyon kasar Sin Wang Gengnian ya yi jawabin cewa, fara watsa labaru a Beibu Bay na da ma'anar ishara ga gidan rediyon CRI da aikin watsa labaru ga ketare. Wannan ya samar da sabuwar hanyar hadin gwiwa tsakanin kafofin yada labaru na tsakiya da na yankunan kasar.

Dadin dadawa, a wannan rana, mataimakin shugaban hukumar kula da watsa labaru da fina-finai da telibijin ta kasar Sin Tian Jin ya halarci bikin tare da sanar da fara watsa labaru a Beibu Bay a hukunce. Kuma jami'an kananan ofisoshin kasashen Vietnam da Cambodia da na Thailand a birnin Nanning sun halarci bikin. Bayan haka, tashar internet ta Beibu Bay mai adreshin www.bbrmedia.com da gidan rediyon jama'ar jihar Guangxi ya kafa ta fara aiki a wannan rana.(Fatima)