Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-22 18:20:29    
Kasar Sin ta tura rukunin masu aikin sa kai a karo na farko zuwa kasar Nijer

cri

Kasar Sin ta tura rukunin masu aikin sa kai a karo na farko zuwa kasar Nijer, rukunin ya hada da samari 14, da za su samar da hidima a kasar Nijer a tsawon shekara daya, kuma za su gudanar da ayyukan koyar da sinanci da koyar da ilmin fasahohin aikin gona da kiwon lafiya da koyar da ilmin yin amfani da kwamfuta.

A ran 22 ga wata da yamma, a birnin Nanjing na lardin Jiangsu, an yi bikin tura rukunin na masu aikin sa kai. Daga cikinsu wanda ya fi yawan shekaru yana da shekaru 30 da haihuwa, kuma mafi kankantar shekarun yana da shekaru 20 ne da haihuwa.

Bisa bukatar da kwamitin tsakiya na kungiyar samari 'yan kwaminis da ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin nuna, tun daga shekarar 2007, lardin Jiangsu ya fara gudanar da aikin tura rukunin masu aikin sa kai zuwa kasashen waje, ya zuwa yanzu, ya riga ya tura rukunoni biyu zuwa ga kasar Guyana. Wannan ne rukuni a karo na farko da kasar Sin ta tura zuwa Nijer, kuma shi ne karo na farko da lardin Jiangsu ya tura masu aikin sa kai zuwa kasashen Afirka.(Abubakar)