Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-22 15:00:28    
Tattalin arzikin Sin ya karu da kashi 7.7 bisa 100 a cikin watanni 9 da suka wuce

cri

A ran 22 ga wata, hukumar kididdiga ta bayyana cewa, tattalin arzikin Sin ya karu da kashi 7.7 bisa 100 a cikin watanni 9 da suka wuce. A kwanan baya, a gun taron manema labaru da ofishin kula da yada labaru na kwamitin gudanarwa na Sin ya yi, kakakin hukumar kididdiga ta Sin Li Xiaochao ya furta cewa, ko shakka babu an tabbatar da cewa, GDP na kasar Sin zai karu da kashi 8 bisa 100 a wannan shekara.

Tun farkon wannan shekara, kasar Sin ta sami ci gaba mai kyau wajen shawo kan matsalar hada-hadar kudi ta hanyar daukar matakai a jere, haka kuma, tattalin arzikin Sin ya fara farfadowa, kuma GDP ya karu da sauri.

Bisa kididdigar da aka bayar, an ce, a cikin watanni 9 da suka wuce na bana, yawan kayayyakin da masana'antu ke samarwa ya karu sosai, bugu da kari, an daina samun raguwar ribar da masana'antu ke samu, kuma an kara zuba jari gare su, haka kuma kudin da jama'a ke samu ya sake karuwa, ban da wannan kuma, yawan kayayyakin da ake sayarwa ya karu da sauri.(amina)