Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-19 18:42:06    
An kafa cibiyar nazarin taron dandanlin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afrika

cri

A ranar 18 ga wata, an kafa cibiyar nazarin taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afrika a kwalejin nazarin kasashen Afrika ta jami'ar horar da malamai ta lardin Zhengjia na kasar Sin. Masana da kwararru a fagen kimiyya sama da 50 da suka fito daga cibiyoyin nazarin kasashen Afrika na yankunan daban daban na Sin da wasu jami'an gwamnatin sun halarci bikin kafa wannan cibiya, kana sun yi tautaunawa mai zurfi kan dangantakar da ke tsakanin Sin da kasashen Afrika.

A cikin shekaru da dama da suka gabata zuwa yanzu, dangantakar da ke tsakanin Sin da kasashen Afrika na bunkasa cikin hanzari, cibiyoyi da dama na kasar Sin na kokarin nazarin dangantakar da ke tsakanin Sin da kasashen Afrika. Babban direkta na wannan cibiya Shehun malami Liu Hongwu ya bayyana cewa, ta kafa wannan cibiya, a hannu daya, za a iya yin nazari kan muhimman abubuwa na hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afrika. A dayan kuma, za a kara yin amfani da sakamakon da aka samu wajen raya dangantakar a tsakanin Sin da kasashen Afrika, don ba da ra'ayoyi wajen bunkasa dandalin tattaunawa cikin dogon lokaci.

A wannan rana, an fara dab'in littafin "Hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika cikin shekaru 50 da suka gabata" a jami'ar horar da malamai ta lardin Zhejiang, kuma a cikin wannan littafi, an hada da sakamakon nazarin da aka samu na hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afrika, kuma an waiwayi tarihin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afrika cikin shekaru 50 da suka gabata. Bisa labarin da aka bayar, an ce, za a bayar da wannan littafi ga wakilan da za su halarci taron ministoci na dandanlin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afrika a karo na 4 da za a yi a kasar Masar.(Bako)