Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-16 21:00:27    
An kaddamar da gasar wasannin motsa jiki a karo na 11 ta kasar Sin a birnin Jinan

cri

A ranar 16 ga wata da dare, an kaddamar da gasar wasannin motsa jiki a karo na 11 ta jamhuriyar jama'ar kasar Sin a birnin Jinan da ke lardin Shangdong a kasar Sin. Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya halarci bikin kaddamar da wannan gasa, kuma ya sanar da bude gasar.

Gasar wasannin motsa jiki ta Sin da ake yi a bayan shekaru 4 ta kasance wata babbar gasar wasannin da suka shafi dukkan wasanni a kasar Sin. Gasar wasannin motsa jiki da ake yi na wannan gami ta kunshi dukkan wasannin motsa jiki na Olympic, cikin har da wasanni 360 da gasanni 33, kuma za a yi dukkan wadannan wasanni ne a cikin birane 17 a lardin Shangdong. 'Yan wasanni sama da dubu 10 da suka fito daga larduna 31 da jihohi masu cin gashin kansu da birane masu zaman kansu da yankin musamman na Hongkong da Macau da kwamitin gasar wasannin motsa jiki na Sin za su halarci wannan gasar, kuma yawan mutanen da suka halarci wannan gasa da yawan wasannin da za a yi sun kafa tarihi a cikin dukkan wasannin motsa jiki na kasar Sin, kuma za a kammala dukkan gasar wasanni a ranar 28 ga wata.(Bako)