Ma Zhaoxu, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ya bayyana a ran 15 ga wata a birnin Beijing, cewar za a kira taron ministoci a karo na hudu na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da kasashen Afirka a kasar Masar a farkon watanni goma na wata mai zuwa. Kuma ya nuna cewa, taron zai taka muhimmiyar rawa da kara sa kaimi ga bunkasuwar dangantaka a tsakanin Sin da kasashen Afirka, da kuma inganta hadin kan bangarorin biyu a fannoni daban daban.
Ma Zhaoxu ya kuma bayyana cewa, muhimmin aiki na taron shi ne kimanta yadda ake gudanar da matakan da aka yi alkwarin daukarsu a yayin taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar, da kuma tsara shiri ga ayyukan hadin kan Sin da kasashen Afirka daga dukkan fannoni a shekaru uku masu zuwa. Kasar Sin tana son kara tuntubar dimbin kasashen Afirka, da kuma yin hadin kai tare da su domin aiwatar da kyawawan sakamakon da aka samu a yayin taron koli na Beijing, da kuma kira taron ministoci a karo na hudu na dandalin tattaunawar yadda ya kamata, ta yadda za a iya inganta hadin kan Sin da kasashen Afirka zuwa wani sabon mataki.(Kande Gao)
|