Musulman kasar Sin dubu 12.7 za su je kasar Saudiyya a bana don yin aikin Hajji, adadin ya fi na bara da dari 7, tawagar maniyyata ta farko za ta tashi a karshen watan da muke ciki.
Mataimakin shugaban kungiyar addinin musulunci ta kasar Sin kuma shugaban tawagar maniyyata Yang Zhibo ya bayyanawa 'yan jarida a ran 15 ga wata cewa, musulman da za su yi aikin Hajji a bana sun zo ne daga larduna da birane 27 a kasar Sin, kuma yawan maniyyata daga jihar Xinjiang ya wuce dubu 3, wanda ya zama matsayin koli a kasar.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, tawagar za ta tashi daga kasar Sin cikin rukuni-rukuni tun daga ranar 30 ga watan Oktoba zuwa ranar 17 ga watan Nuwamba, bayan da suka kammala yin aikin Hajji, za su komo kasar Sin cikin rukuni-rukuni tun daga ranar 3 zuwa 21 ga watan Disamba.(Zainab)
|