Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-14 10:17:34    
Firaministan Sin da na Rasha sun halarci bikin murnar ranar cika shekaru 60 da kulla huldar diplomaciyya tsakanin Sin da Rasha

cri
A ran 13 ga wata da dare, a babban dakin taron jama'a dake birnin Beijing na Sin, an yi gagarumin bikin murnar ranar cika shekaru 60 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Rasha, kana bikin rufe aikin "Shekarar harshen Rashanci na kasar". Firaministan Sin Wen Jiabao da takwaran aikinsa na Rasha Vladimir Putin dake ziyara a Sin da sauran mutane 3000 na sassa daban daban daga kasashen biyu sun halarci wannan taro.

A cikin jawabansu, firaministoci na kasashen biyu sun waiwaya shekaru 60 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu, kuma sun nuna babban yabo ga nasarorin da aka samu ta hanyar kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakaninsu, da zumunci mai zurfi irin na gargajiya tsakanin jama'ar kasashen biyu. Bangarorin biyu sun bayyana cewa, a matsayin kasashen dake makwabtaka da juna kana manyan kasashe da kuma zaunannun membobin kwamitin sulhu na MDD, kamata ya yi Sin da Rasha su kara amincewa da juna a fannin siyasa, da zurfafa hadin gwiwar samun moriyar juna bisa manyan tsare-tsare, a yunkurin ba da karin gudummawa wajen sa kaimi ga shimfida zaman lafiya na duniya da bunkasuwar kasa da kasa baki daya.

Bayan haka kuma, firaministocin kasashen biyu sun kalli wasannin da masu fasahohi daga kasashen biyu suka nuna tare da wasu mutane masu kokarin sada zumunta na sassa daban daban.

Kafin bikin murna kuma, firaministocin kasashen biyu sun ba da lambobin yabo ga wadanda suka sami nasara a gasar "Sinawa sun rera wakokin Rasha" da gidan rediyon kasar Sin ya shirya, da wadanda suka ba da babbar gudummawa a fannin koyar da harshen Rashanci a kasar Sin.

Dadin dadawa, a wannan rana, Wen Jiabao da Vladimir Putin sun gana da wakilan 'yan kasuwa na kasashen biyu dake halartar dandalin tattaunawar koli na sassan masana'antu da cinikayya da tattalin arziki na Sin da Rasha a babban dakin taron jama'a dake birnin Beijing na Sin. Kuma bayan da suka ba da jawabai, firaministocin kasashen biyu sun saurari ra'ayoyi da shawarwarin da 'yan kasuwa suka bayar don karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannin tattalin arziki da cinikayya. Kuma sun sa kaimi ga kamfanonin Sin da na Rasha da su kara hada gwiwa, a yunkurin sa kaimi ga hadin gwiwarsu a wadannan fannoni zuwa wani sabon mataki.(Fatima)