Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-14 09:41:43    
An bude nunin litattafai na Frankfurt a 2009

cri
A ran 13 ga wata da yamma, an bude bikin nunin littattafai na Frankfurt na 2009 na tsawon kwanaki 6 a cibiyar nune-nune ta Frankfurt. Mataimakin shugaban kasar Sin Xi Jinping da firayim ministar kasar Jamus Madam Angela Merkel da shugaban jihar Hessen ta Jamus Roland Koch da magajiyar garin Frankfurt Madam Petra Roth duk sun halarci bikin.

Kasar Sin dake kan matsayin wata kasa babbar bakuwa ta 22 ta halarci bikin nunin littattafan, kuma ta gudanar da ayyuka da dama, ciki har da bikin bude nunin da na kide-kide na kasar da ta kasance babbar bakuwa da sauransu.

Xi Jinping ya yi jawabi a bikin, inda ya furta cewa, kasar Sin ta halarci bikin nunin littattafai na kasa da kasa ne a matsayin kasa babbar bakuwa, wannan ya samar da zarafi ga kasar Sin domin ganin al'adun duniya wanda kuma ya samar da zarafi ga kasashen duniya domin ganin al'adun kasar Sin masu kyau.

Bugu da kari, kasar Sin tana fatan gabatarwa duniya al'adunta ta hanyar bikin nunin litattafan, kuma tana fatan gabatarwa duniya bunkasuwar da sha'anin dab'in littattafai na Sin ya samu da koyar darasi daga ci gaban da sha'anin dab'in littattafai na kasashe daban-daban suka samu ta yadda za a kara yin musayar ra'ayi da hadin kai.(amina)