Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-13 15:23:22    
Kasar Sin za ta dauki matakai masu amfani wajen kiyaye kayayyakin al'adun gargajiya na tarihi da aka gada daga kaka da kakanni

cri
A ran 13 ga wata a nan birnin Beijing, shugaban sashen kula da harkokin kayayyakin al'adun gargajiya na tarihi da aka gada daga kaka da kakanni na hukumar al'adu ta Sin Mr Ma Wenhui ya furta cewa, ya zuwa yanzu, an shigar da ayyuka guda 29 na Sin cikin takardar jerin sunayen kayayyakin al'adun gargajiya na tarihi da aka gada daga kaka da kakanni na dan Adam ta hukumar UNESCO ta MDD, wannan ya bayyana cewa, hukumar UNESCO ta MDD da kasashen duniya suna amincewa da ayyukan kiyaye kayayyakin al'adun gargajiya na tarihi da aka gada daga kaka da kakanni da Sin take yi. A matsayin kasar da ta fi mallakar kayayyakin al'adun gargajiya na tarihi da aka gada daga kaka da kakanni, kasar Sin za ta cika alkawarinta na yin kokarin daukar matakai domin kiyaye wadannan kayayyakin tarihi masu daraja.(amina)