Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-12 15:37:43    
Babban shugaban kamfanin yada labaru na kasar Tanzania ya ziyarci gidan radiyon kasar Sin

cri
A ran 12 ga wata, babban shugaban kamfanin yada labaru na kasar Tanzania Todi Mhando ya ziyarci gidan radiyon kasar Sin wato CRI, inda ya yi shawarwari da mataimakin shugaban CRI Wang Yunpeng kan batun watsa shirye-shiryen CRI a kasar Tanzania.

Mista Todi Mhando ya bayyana cewa, a shekarun baya, gidan radiyon kasar Sin ya samu babban ci gaba a kasashen Afrika, kuma ya ba da babbar gudummawa wajen ci gaba da yin mu'ammalar tattalin arziki da al'adu a tsakanin Sin da Afrika da dai sauransu.

Bugu da kari, mista Mhando ya furta cewa, zumuncin dake tsakanin Sin da Tanzania yana da dogon tarihi, kuma yana da zurfi. Kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu za ta ingiza hadin gwiwa dake tsakanin kamfanin yada labaru na Tanzania da CRI.

Mataimakin shugaban gidan radiyon kasar Sin Wnag Yunpeng ya amince da shawarwarin da bangaren Tanzaniya ya bayar, kuma ya tattauna da mista Mhando kan wasu ayyuka na zahiri game da watsa shirye-shiryen CRI a kasar. Ban da haka kuma, ya bayyana cewa za a gaggauta tabbatar da watsa shirye-shirye a kasar.(Asabe)