A ran 12 ga wata, bisa labarin da hukumomin da abin ya shafa suka bayar, an ce, a lokacin hutu na bikin kafuwar sabuwar kasar Sin na tsawon mako daya, yawan masu yawon shakatawa da jihar Tibet ta karba ya kai kimanin dubu 300 kuma wanda ya kai miliyan 4.7 ko fiye a watanni 9 da suka wuce, haka ya sa yawan masu yawon shakatawa da jihar Tibet ta karba a wannan shekara ya kai sabon matsayi a tarihi.
A shekarar 2007, yawan masu yawon shakatawa da jihar Tibet ta karba ya kai miliyan 4, wanda ya taba kaiwa matsayi na daya a tarihi.(amina)
|