Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-12 09:56:02    
Xi Jinping ya ziyarci cibiyar al'adun kasar Sin dake Berlin

cri
A ran 11 ga wata, yayin da yake ziyartar cibiyar al'adun kasar Sin dake birnin Berlin, mataimakin shugaban kasar Sin Xi Jinping dake ziyara kasar Jamus ya bayyana cewa, ya kamata a yi amfani da cibiyar da kyau don yada al'adun Sin mai dogon tarihi ga jama'ar kasar Jamus da ta Turai, ta yadda za a ci gaba da mu'amala da hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Jamus, da kuma Turai.

Mista Xi Jinping ya nuna cewa, tarihin al'adun kasar Sin yana da shekaru dubu biyar, kamata ya yi a yi amfani da wannan cibiya da kyau don ba da gudummawa ga dangantakar dake tsakanin Sin da Jamus da kuma Turai.

Ban da haka kuma, mista Xi Jinping ya ziyarci bikin nune-nune na mutanen Sin dake karatu a Jamus don murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin, da ajin karanta litattafi na yara, da kuma ajin rawa, kana da ajin koyar da Sinanci wadanda cibiyar al'adu ta yi. Kuma ya zo dandalin tattaunawar adabi na Sin da Jamus da ake yi a cibiyar, inda ya yi hira da masana ilimin al'adun Sin da na fassara na kasar Jamus a kan bunkasuwar adabi na kasashen biyu da mu'ammalar dake tsakaninsu.

Yayin da yake a kasar Jamus, mista Xi Jinping zai yi shawarwari da shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel, kuma zai halarci bude bikin nune-nunen litattafai na Frankfurt da dai sauransu.(Asabe)