Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-09 12:15:58    
Kamata ya yi kafofin watsa labaru na kasa da kasa su ba da gudummawa don kafa wata duniya mai jituwa

cri

A ran 9 ga wata, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya yi wani jawabi yayin bikin kaddamar da taron koli na kafofin watsa labaru na duniya, inda ya bayyana cewa, kamata ya yi kafofin watsa labaru na kasashen duniya su yi kokarin ba da gudummawa don kafa wata duniya mai dauwamammen zaman lafiya da wadata bisa ra'ayin samun bunkasuwa da kasa da kasa suka amince da shi.

Hu Jintao ya nuna cewa, a halin yanzu dai, kafofin watsa labaru sun kara yin tasiri a kowace rana ga duniya a fannonin siyasa da tattalin arziki da zamantakewar al'umma da al'adu da dai sauransu, kana sun yi tasiri ga mutane a fannonin tunani da aiki da zaman rayuwa da dai sauransu. Kamata ya yi kafofin watsa labaru na kasa da kasa su yi amfani da fifikonsu, da yada tunanin zaman lafiya da bunkasuwa da hadin gwiwa da samun moriyar juna da hakuri da juna, da watsa labaru kan hakikanin halin da ke kasancewa na dogara da bangarori da yawa a duniya da aiwatar da tsarin bai daya a duniya a fannin tattalin arziki da kuma wayewar kai a fannoni daban daban a duniya, da bayyana halin bunkasuwa na kasashen duniya, da kuma sa kaimi ga kasashe masu tasowa da su samu ci gaba.

Hu Jintao ya ce, gwamnatin Sin ta nuna goyon baya ga kafofin watsa labaru na kasar Sin da su kara yin mu'amala da hadin gwiwa tare da kafofin watsa labaru na kasashen ketare a fannonin watsa labaru da neman samun gwanaye da fasahohin sako da kuma bunkasa ayyuka. Kuma yana fatan kafofin watsa labaru na kasashen duniya za su ba da sabuwar gudummawa don kara fahimtar juna tsakanin Sin da sauran kasashen duniya, da zurfafa zumunci tsakanin jama'ar kasashen duniya da ta kasar Sin.(Zainab)