Ran 16 ga wata da safe, a nan birnin Beijing, an kaddamar da bikin mika wutar yola ta gasar wasannin motsa jiki ta duk kasar Sin a karo na 11, inda Wu Bangguo, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya kunna wutar yola ta gasar, ta haka a hukumance ne aka kaddamar da harkar mika wutar yola ta gasar wasannin motsa jiki ta duk kasar Sin a karo na 11 mai babban take kamar haka "Nuna wa kasar Sin fatan alheri tare da jin dadin gasar wasannin motsa jiki ta duk kasar".
A bikin da aka yi a yau, kungiyoyi 5 na masu mika wutar yola ta gasar sun kaddamar da tafiyarsu ta mika wutar yolar a duk fadin kasar Sin a hukumance. Ko da yake an yi ruwan sama kadan a nan Beijing, amma harkar mika wutar yolar ta jawo hankalin dubban mazauna birnin Beijing.
Za a yi gasar wasannin motsa jiki ta duk kasar Sin a karo na 11 a ran 16 ga watan Oktoba a wannan shekara a lardin Shandong, wadda gasa ce mafi girma kuma mafi koli da za yi a kasar Sin bayan gasar wasannin Olympic ta Beijing.(Tasallah)
|