Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-08-08 16:30:20    
Gasar wasannin Olympic ta sanya Beijing ya kai wani sabon mataki wajen neman ci gaba

cri
Lokacin da ake murnar cika shekara 1 da shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing, Mr. Liu Qi, sakataren reshen kwamitin Beijing na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kungiyar Beijing ta ingiza raya ci gaban biranen da suka shirya gasar wasannin Olympic ya bayyana cewa, gasar wasannin Olympic ta sanya Beijing ya kai wani sabon mataki wajen neman ci gaba.

A gun taron dandanlin tattaunawar ci gaban biranen da suka taba shirya gasar wasannin Olympic da aka yi a birnin Beijing, Mr. Liu Qi ya ce, lokacin da aka yi gasar wasannin Olympic a Beijing, an soma aiwatar da ma'aunai fiye da dubu 4 da suke da nasaba da fannoni 13, ciki har da ingancin abinci da tabbatar da ingancin muhalli da zirga-zirga da tabbatar da tsaron jama'a da dai sauransu bisa bukatun da ake da su a gun gasar. Ya zuwa yanzu, wadannan ma'aunai sun zama ma'aunan da birnin Beijing yake bi a kullum a kai a kai domin tafiyar da harkokin birnin kamar yadda ya kamata.

Mr. Liu ya ce, birnin Beijing ya kara saurin samar da ayyukan yau da kullum, kamar tsarin zirga-zirga na zamani bayan gasar.

A waje daya, birnin Beijing ya ci gaba da kyautata tsarin masu aikin sa kai domin ci gaba da ba da kyakkyawar hidima ga zaman al'umma. Haka kuma, ayyuka marasa shinge da ake samarwa nakasassu sun samu karuwa da kuma kyautatuwa a birnin. Bugu da kari kuma, yawan mutanen da suka soma motsa jiki a kullum ya samu karuwa sosai. (Sanusi Chen)