Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-08-07 10:26:03    
An yi bikin kida da wake-wake na murnar cika shekara daya da gudanar da wasannin Olympics a birnin Beijing

cri

A ran 6 ga wata da dare, a filin da aka san shi da sunan Olympic Green da ke birnin Beijing, an yi bikin kida da wake-wake na murnar cika shekara daya da gudanar da wasannin Olympics a nan birnin Beijing.

Mutanen gida da na waje fiye da 5000 sun halarci bikin, ciki har da Liu Qi, shugaban kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing, da tsohon shugaban kwamitin kula da wasannin Olympics na Beijing, Hein Verbruggen.

A cikin jawabinsa, Mr.Liu Qi ya ce, a ran 8 ga watan Agusta na shekarar da ta gabata, yayin da aka kunna wutar wasannin Olympics a birnin Beijing, mafarkin al'ummar kasar Sin ya zama gaskiya. Bisa manufar gudanar da wasannin Olympics da ke da muhalli mai kyau da fasahohin zamani da kuma al'adu nagari, birnin Beijing ya gabatar wa duniya wasannin Olympic masu kyau da ba a taba ganin irinsu ba, haka kuma ya shaida wa duniya wata sabuwar kasar Sin da ke da dimokuradiyya da budadden tunani da kuma ci gaba.

Mr.Liu Qi ya kara da cewa, kamata ya yi a zaunar da ruhin wasannin Olympic a birnin Beijing, don ya amfana wa birnin na Beijing har abada.(Lubabatu)