Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-07-28 15:41:18    
Lambun shan iska na Olympic na birnin Beijing ya zama abin tinkaho na yawon shakatawa bayan gudanar da wasannin Olympic na birnin Beijing

cri
Bisa sabbin alkaluman da hukumar yawon shakatawa ta birnin Beijing ta bayar a ran 28 ga wata, an ce, a cikin watanni 6 da suka gabata na shekarar bana, sana'ar yawon shakatawa ta samu bunkasuwa sosai a birnin Beijing, kuma yawan mutanen da suka yi yawon shakatawa da yawan kudin da aka samu wajen sana'ar yawon shakatawa sun karu.

Daga cikinsu, dakunan wasannin Olympic na kasar Sin sun ba da gudumawa ga bunkasuwar sana'ar yawon shakatawa na birnin Beijing bayan gudanar da wasannin Olympic. Yanzu, yawan mutanen da suka yi yawon shakatawa a lambun shan iska na Olympic na birnin Beijing ya kai dubu 60 zuwa dubu 70 a ko wace rana.

Darekatan sashen kula da manyan ayyukan lambun shan iska na Olympic na birnin Beijing Su Yan ya bayyana cewa, lambun shan iska na Olympic dake hada da dakunan wasannin Olympic ya hada da karin al'adu.

Ban da gine-gine wasannin Olympic wato Bird's nest da water Cuber da sauransu, lambun shan iska na Olympic ya kara samar da filayen yawon shakatawa ga masu sha'awar yawon shakatawa.

A sa'i daya kuma, lambun shan iska na Olympic yana yin kokari wajen ba da hidima ga mazaune yankunan da ke dab da lambun.(Abubakar)