Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-05-07 16:58:44    
Ana gudanar da aikin sake gina lardin Sichuan bayan bala'in girgizar kasa kamar yadda ya kamata

cri

A ran 7 ga wata, wakilinmu ya samu labari daga taron manema labaru domin tunawa da zagayowar ranar cika shekara guda da faruwar girgizar kasa a gundumar Wenchuan a ranar 12 ga watan Mayu na shekarar 2008 cewa, yanzu, ana gudanar da aikin sake gina lardin Sichuan bayan bala'in girgizar kasa kamar yadda ya kamata.

Kakakin gwamnatin lardin Sichuan Yu Wei ya bayyana cewa, za a kammala aikin gina gidajen manoma a yankin da aka yi fama da bala'in girgizar kasa kafin karshen wannan shekara, kuma za a kammala gina gidajen mutanen birane da garuruwa kafin watan Mayu na shekara mai zuwa. Yanzu an riga an soma ayyukan kafa makarantun da bala'in ya lalata kashi da 73.3 cikin kashi dari a yankuna 39 da girgizar kasa ta fi yi wa illa, zuwa lokacin bazara na shekarar badi, dukkan dalibai za su yi karatu a cikin sabbin gine-ginen makarantu. Dadin dadawa, an tabbatar da cewa za a kammala manyan ayyukan kyautata rayuwar jama'a na kashi 99 cikin kashi dari a cikin shekaru 2 masu zuwa, kamar ayyukan kiwon lafiya da sauransu.

Ban da wannan kuma, shugaban hukumar kudi ta gwamnatin lardin Sichuan Huang Jinsheng ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, lardin Sichuan ya samu kudin taimako da yawansu ya kai RMB Yuan biliyan 15 da miliyan 750 da mutanen sassa daban daban na zaman al'umma suka bayar, kuma an riga an yi amfani da wadannan kudin RMB Yuan fiye da biliyan 10 da miliyan 200. Za a sanar da yadda aka yi amfani da kudin a kan shafin internet na gwamnatin lardin Sichuan.(Lami)